Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

 


 

Sanarwa!!!

 

Bisa yawan wasikar da muke samu ta neman taimakon 'Karin bayani kan yadda za'a gina shafin yanar gizo, daga masu wanda muka ba filin kansu domin giina shafin yanar gizo a wannan fili na www.gumel.com, baza mu iya amsawa kowa da wasikar sa ba domin yawan wasikon da muke samu a kowace rana.

Saboda haka, muna farin cikin sanad da kuwa kan a halin yanzo muna 'Ko"karin gina wani shafin zauran shira, wanda cikin wannan zauren kuwa zai buga tasa tambayar, kuma zamu rika amsa tambayoyen naku cikin kwana daya, kuma ta wannan hanyar idan akwai wanda suke da sanin amsar tambayar kokuma suka san hanya mafi sauki masu sha'awar taimakawa mutanan mu cikin harshen Hausa zasu iya bada nasu 'Karin bayanin.

Ta wannan hanyar sauran mutane zasu iya 'Karuwa daga tambayar ku da kuma amsoshen da aka bayar.

A cikin wanan zauren dukkan Hausawa masu sha'awar zama Webmaster da kuma masu 'Kokarin koyan gina shafin yanar gizo za su san juna, da kuma 'Karawa juna ilimi cikin harshen mu na Hausa, idan akwai wani abu wanda bamu fashin taba cikin harshen turanci sai muyiwa juna bayani cikin harshen mu.

Da yardar Allah nan bada jumawa zamu gama aikin wannan shafin, masu tambaya karku zaci mun manta daku, kuna cikin zuciyar mu, kuma saboda yawan ku, bazamu yi sankai mu amsa wasu muki amsawa sauran.

 

Babu Batsa cikin wannan shafi, dokkan wanda muka ba fili cikin wannan yanar gizo, bazai sa kayan tsiraice ba, babu 419, bazaka saida komai ba.


A Halin yanzu muna cikin aikin tsara wannan shafin, sabo da haka a halin yanzu zaku iya aiko mana da wasika hade da wadannan bayanan domin mu bude muku filin ku na yanar ziro.

Zamu baku kyautar fili cikin uwar garken mu 10m domin ku tsara shafin ku na internet, shi wannan shafin zai zamunto cikin sunan ku kamar haka www.sunanka.gumel.com, watau idan sunan ka Ibrahim shafin ka zai zama www.ibrahim.gumel.com, wannan hanyar zata kai kowa cikin shafin ku.

Ku aiko mana da wasika ta [email protected] da wadanan bayanan

1. Suna ku
2. Kasar da kake zaune
3. Garin ku
4. Makarantar da kake idan dan makaranta ne ko gurin aikin ku
5. Sunan da kake so na yanar gizo, watau www.sunanka.gumel.com
6. Irin abinda zaka sa cikin shafin ka.
7. Aderishin ku da lambar waya.
8 Karin bayani a kan ku domin
9. email wanda zamu aiko maku da bayani kan yadda zaku shiga shafin ku.

[email protected]

Da zarar mu samu wasikar ku, ciki da abinda muka tambaya zamu rajista na sunan ku, mu aiko maku da bayani kan yadda zaku shiga shafin ku da kuma karin bayani kan yadda zaku gina shafin ku.

 

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka [email protected]

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.