|
|
Tsarin
Aiki
|
Tsarin aiki ga Malamin Makarantar Firamare shine
ginshikin aikin da zai koyar a kowace rana. Wajibi ne ga Malami
ya tsara aikinsa daki-daki kuma yaje cikin aji da tsarin aikin
a rubuce. Rashin zuwa da tsarin aiki Makaranta yana batawa Malamai
daraja da rage masu kwazo. Kamar Manomi ne yaje gona babu fatanya,
ko dan kasuwar da bashi da jari. Malamin makaranta baya cika
Malami sai ya san abinda zai koyar, da sanin yadda zai tsara
aikin nasa domin ya dace da hankalin yaransa ta yadda zasu fahimta.
Hanyar koyarwa kamar jagora ce ga Malami. Hanyoyin koyarwa sun
kuma bambanta amma ga wadda aka tsara cikin wannan karamin littafin
don yiwa Malamai sabun shigajagora. Idan Malami zai tsara aikinsa
a littafi sai ya fara da wadannan:
1. Kwanan wata
2. Sunan Ajin da za'a koyar.
3. Me za'a koyar a wannan rana?
4. Manufar abinda za'a koyar. Malam ya tambayi kansa cewa menene
amfanin abinda za'a koyar a wannan rana?
5. Somin tabi, wato Malami ya jawo hankalin yaransa da farko
da wani abu wanda zai sa su saurare shi kafin ya shiga cikakken
aiki.
6. Aikin kansa. A nan ana bukatar Malami ya rubuta irin abubuwan
da zai koyawa yaransa a cikin littafinsa na tsarin aiki daki-daki.
Misali daga wannan abu sai kuma wannan. Sai kuma Malami ya aikata
abinda ya tsara a cikin aji. Kada Malami ya rubuta tsarin aiki
ya shiga aji yayi zamansa kawai ba tare yabi tsarin ba.
7. Kayan aiki. Ana son Malami ya rubuta sunayen duk abubuwan
da zai yi amfani dasu a cikin aji wajen koyarwa, ya kuma je
dasu Makaranta sannan yayi amfani dasu yadda ya dace. Ba'a son
Malami ya kai kayan aiki ajinsa ya jibge kawai, kila ma shi
kansa bai san amfaninsu ba, ya kaisu ne don yaudarar Sufeton
duba Makaranta.
|
|
{talla} |
|
|
|