|
Musulunci shine addinin mafi yawan al'umrnar
Hausawa. Shi kuVa addinin Musulunci yana da nasa tsarin ilimi
wanda kuma Hausawa ke bi kafin zuwan turawa 'yan mulkin mallaka
wadanda suka kawo nasu tsarin da ake kira ilmin Boko. Bisa
ga tsarin farko kafin zuwan turawa, yara tun tun suna "yan
shekara hudu ko biyar suke fara zuwa makarantar Allo inda
kowane Almajiri yakan fara karatun Babbaku, sannan yaje na
Farfaru. Idan ya gama Farfaru sai ya kama Hajjatu. Daga nan
kuma sai ya fara Hadda, idan hadda ta nuna sai ya fara karatu
dabita.
Darajar Almajirci hawan-hawa ce. Akan fara da zama Kolo, ko
Titibiri, da^a nan sai a zama Gardi. Idan Gardi ya rika yakan
zama Malam ko Mai Darasu. Daga Mai Darasu sai a koma matsayin
Likari. Idan Likari ya ya rika sai ya zama Gwani kafin ya
hau Karagar Babban Malami wanda aka t'i sani da sunan Alaramma.
Darajar kokoliya ita ce ta Shaihun Malami. Akun dauki karatu
a Makaranta, ko Tsangaya ko Kiskadi a wajen masu bada karatu.
Ga kuma yadda sigar Makarantar Allo take.
|
|