|
Amshin wannan waka shi ne
(Mamman jikan Audu)
A lokacin da aka yi hira da Alhaji Mamman shata a gidajen
rediyo c Telbijin a Nigeria da Amirka, an tambayeshi wace
waka yafi so a ra sai yace wakoki biyu. Bakandamiya da wakar
bashar Sarkin daura Amma duk da haka bai yi wannan waka ta
»arkin Daura da tsaho 1 wadda kuma a jerin wannan littafi
ita ce ta farko. Rashin tsahon ws waka ta farko ya faru ne
saboda ganin cewa Alhaji Mamman Shata riga ya wake Alhaji
Muhammadu Bashar lokacin da yake Wamban Bari mu duba wakar
da ya yiwa Sarkin daura tarfarko.
Mamman Jikan Audu.
Mahmman dan Mamuda
Mamman Jikan Audu.
Giwa ikon Allah, Mamman kogi ikon Allah
giwa bukkar daji.
Mamman Jikan Audu.
Kogi ikon Allah
Mamman Jikan Audu.
Mamman kogi ikon Allah.
Mamman Jikan Audu.
Yara daji ya kai daji
daga giwa sai lya 'yanta
sai Zaki ke yawo, sai 'ya'yan kyar-kyece.
MAMMAN JIKAN AUDU.
Daura birnin Mamman
daga zaki sai 'ya 'yan kyar-kyace.
Mamman Jikan Audu.
Mamman ayi a gama sai doki.
Mamman jikan Audu.
Kai manya-manya inji kanana
jure fari sai tofa- wuyar wuta sai karfe,
ayi a gama sai doki, ga wata rigima ba
mai maganinta sai dai Allah.
Mamman Jikan Audu.
Ga wani rikicin ba mai
warware shi sai dai Allah.
Mamman Jikan Audu.
Mamman ayi a gama sai doki.
Mamman jikan Audu.
|
|