|
|
Bayani
Kan Wakokin Mata
|
Yawancin mawakan Hausa kafin su fita filin waka
ko wasa, su kan shirya wakar da zasu yi a gida domin tabbatarwa
tare da yaransu wato masu amshin waka don kaucewa kuskure. Amma
Alhaji Mamman Shata ya bambanta da sauran mawaka ta wannan fannin.
Wakarsa zuwa take kamar mahaddacin waka ne, kuma wani abin mamaki
shine da mai kada masa kalangu da su kansu 'yan amshinsa da
zarar Alhaji Mamman Shata ya fara waka sai aji kida da amshi
sun tafi tare da wakar. A lokacin da ya sauka a Daura kamar
yadda ya nuna cikin wakarsa ta mai martaba sarkin Daura, bai
tsaya yayi wani bincike a kan tarihin matar sarkin Dauran ba,
abinda yayi kawai ya dan yi tunaninsa na tarihin da yaji kakanni
na fadi sai ya fara waka. Daga karshe bayan ya kammala wakar
mai dakin gabas babu wanda ya jawo hankalinsa da cewa yayi kuskure
cikin abubuwan da ya bayyana game da ita. Da kuwa akwai kuskure
da fadawan sarki ne zasu fara yin magana. Idan kuma aka dubi
farkon wannan waka ta mai dakin gabas za'a ga cewa ya kirata
da sunan mai dakin gabas bayan kuwa an san tana da suna. Dalilin
da Alhaji Mamman Shata ya bayar shine bisa ga al'adar hausawa
ladabi ne a boye sunan wanda ake jin kunya tun daga kan iyaye
zuwa manyan kasa. Hikimar da yayi amfani da ita a nan ita ce,
sai kawai ya nemi sanin bangaren da dakinta yake a cikin gidan
sarkin Daura. Dakinta ne daga gabas don haka sai ya kirata mai
dakin gabas. Kuma can wurin da yake cewa duk bafulatanin duniyar
nan, ko na dawa zuwa nan birni, babanta ne ke mulki nai ya nuna
ke nan tana da nasaba da sarauta, wato mai dakin gabas 'yar
sarauta ce a kasar Nijer. A duk lokacin da Alhaji Mamman Shata
ya je gidajen sarakuna don yayi waka, yawanci matan sarakunan
ne ke bashi kayan mata da kudi masu yawa. Dalilin haka cikin
wannan wakar yake cewa zashi wurin uwar dakinsa, mai raba riguna
'yar Iro. Alhaji Mamman Shata yayi wakokin mata masu yawan gaske
kuma fitattu wadanda bamu tsara buga su a wannan littafi a yanzu
ba sai a gaba. Wakokin sun hada da A'i kyaftin diyar nasara.
Barira diyar
|
|
|
|
|
|