|
Kida da waka na nuna halin rayuwar jama'ar da
su makadan da mawakan ike tare dasu. Bambanci tsakanin waka
da wake wato rubutacciyar waka ko kuma kamar yadda masana ke
kiranta da sunan ARULI shine kida. Kayan kidan kansu suna nuna
al'adun mutane. Hikimar dake kunshe cikin ARULI wake kan nuna
himma da karawa mutane kuzari da kaimi wajen kara mmma kan abubuwan
da suke gudanarwa. Wadansu waken kuwa wa'azi suke yi ga jama'a
don bin tafarki wanda ya dace. Misali wakar marigayi Sa'adu
Zungur wadda yayi kan bidi'a inda yake cewa:
Ka daura niyya a kan waka kana addu'a,
A'uzu Billah daga Shaidani a kan bidi'a.
San nan kawo Basmala bisa kan rikon sunna,
kabiya da yin Hamdala ita ce uwar sa'a.
Matsayin wake a kasar Hausa ya fara habaka ne a farkon karni
na goma sha tara lokacin da Shehu Usmanu Dan Fodivo da kaninsa
Abdullahi tare da dansa Muhammadu Bello suka himmatu wajen
rubuce-rubuce don wayar da kan mabiyansu a jihadin da suke
yi. Irin wakokin da suka yi suna nan a rubuce cikin littafm
nan mai suna "Infaqul-Maisur". Wakokin kuma sune
wadanda suka jibanci wa'azi, neman ilmi, ayyukan mulki da
shari'a. Daya daga cikin irin wadannan wake akwai wadda tafi
shahara wadda Abdullahi ya rubuta mai suna "wakar gode
Allah" don nuna godiyarsa ga Allah madaukakin sarki da
ya basu sa'ar yin hijira. Wadannan rubuce-rubuce sun yi sune
cikin ajami. Daga baya, daya daga cikin 'ya'yan Shehu Usmanu
Dan Fodiyo mai suna Isa ya yi kokarin fassara ayyukan Shehu
daga larabci ko fillanci zuwa Hausa musamman ma wakokinsa
na wa'azi, Tauhidi da Fiqhu.
Cikin karni na ashirin wato bayan Turawan mulkin mallaka
sun mamaye kasar Hausa kuma karatun boko ya fara karbuwa sai
aka rubuta wake da boko. A wancan lokacin, Sheikh Na'ibi Sulaiman
Wall wanda a yanzu Alkalin kotun daukaka kara ta musulunci
ne a Kano da kuma marigayi Ma'azu Hadeja wanda a wancan lokacin
Malamin makaranta ne sun shahara wajen rubuta wakoki da Hausar
boko, kuma sun fi maida hankali kan ilmi da addini. A bangaren
wakokin da suka danganci mulki da siyasa kuwa, shahararrun
marubuta da Hausar boko sun hada da marigayi Sa'adu Zungur,
Mudi Sipikin, Akilu Aliyu da marigayi Malam Aminu Kano. Wani
fannin ma bayan ilmi, siyasa da harkokin mulki sun rubuta
wakoki da dama kan yakin basasar kasashen Hausa da yakin duniya
na daya da na biyu. Haka kuma marigayi Sarkin Zazzau Aliyu
Dan Sidi ya rubuta waka kan ziyara mai tarihi da ya kai kasar
Kano cikin 1914. Daga cikin mawakan Hausar boko na wannan
zamani akwai Abubakar Ladan Zariya wanda ya shahara a wakarsa
ta Africa da kuma wakar siyasa. Akwai kuma Awwalu Isa wanda
yayi rawar gani a wakokin siyasar jumhuriyya ta biyu. Marigayi
Yusuf Kantu ba kashin jefarwa bane a fannin wakokin Hausa.
A duk lokacin da aka yi magana kan al'ada cikin wannan littafin
ana magana ne kan abubuwa biyu. Na farko dai akwai al'ada
wadda addini bai yarda da ita ba. Idan ance addini a wannan
littafin ana magana ne kan addinin Musulunci. Daga cikin al'adun
da musulunci bai yarda da su ba akwai wadda ta shafi bautar
wanin Allah wadda Maguzawa ke yi ta hanyar bori. 'Yan zamani
kuma na hada bidi'a a harkokin aure, yin radin suna da jana'iza.
Amma kuma akwai wadansu al'adunmu na gargajiya masu kyau da
musulunci ya yarda da su. Irin wadannan al'adu na gargajiya
kuwa sune irin na rayuwar yau da kullun kamar wadanda suka
danganci cin abinci da hannu bayan an wanke hannun, yin aski
don a rage gashi idan yayi yawa, sanya tufafi wadanda zasu
rufe al'aurar mutun da ziyarar 'yan uwa. Wadannan basu saba
ka'idojin addinin musulunci ba. Addinin musulunci kuwa shine
addinin da bahaushe ya karba hannu bibbiyu. Don haka ashe
wajibi ne ga hausawa su kara himmatuwa wajen ganin matasa
sun yi watsi da al'adun nasara wadanda yanzu ke neman zame
mana kadangaren bakin tulu.
Idan an lura za'a ga matasan mu sun watsar da aradunmu na
gargajiya musamman wadanda suka danganci kida da waka sun
rungumi na turawa, suna zaton yin haka shine burgewa. Ya kamata
a rika tunawa da karin maganar nan ta hausawa dake cewa "kowa
ya bar gida-gida ya barshi". Ba wai lallai bane mu dogara
da kidan kotso, kalangu, Algaita da sauransu ba, muna iya
inganta wadannan kayan kade-kaden da muke dasu na gargajiya
don su dace da zamani ta yadda matasa zasu yi sha'awa. Ana
iya sirkawa da kayan kida irin na zamani kamar yadda mawaka
da makadan "yarabawa" keyi. Haka kuma idan aka dubi
yadda makadan bakaken fatar America suka shahara a filin wakar
zamani za'a ga cewa sun sami damar yin hakan ne ta hanyar
sirka kayan kidan da kakanninsu wadanda aka kai America da
sunan bayi suka tafi dasu daga nahiyar Africa. Yanzu haka
dai bakaken fatar America sun shallake kowa a fllin kida da
wakokin zamani a nahiyar turai. Don haka ya kamata tun daga
makarantun farko da yaran hausawa ke zuwa na zamani, a fara
koya masu muhimmancin kida da waka a al'adun hausawa.
Muhimmancin kowace aPumma shine tsare da kuma inganta al'adunta
na gargajiya masu kyau. Barin al'ada tamkar barin wani ginshikin
tubali ne na ginin halayyar jama'ar wannan al'umma. A yanzu
haka a kasar Hausa an tashi tsaye don inganta al'adun hausawa
domin kuwa tun kafin zuwan turawa an san cewa hauswa suna
alfahari da al'adunsu musamman wadanda suka jibanci sutura
da bukukuwa. Haka kuma an san hausawa da zumunci, misali lokacn
aka yiwa wani rasuwa zaka gansu a wajen jana'iza da zaman
makoki. Haka kuma idan haihuwa aka yi zaka ga jama'a sun taru
a wajen radin suna don u.| dan uwansu murna. Idan kuma muka
duba ayyukan gona za'a ga hadin kai wajen noman gayya. A halin
yanzu kuma ga ayyukan gayya na gyaran gari jama'ar hausawa
ke haduwa suna yi. Koda yake halin matsi na kudi ya tauye
abubuwa masu yawa a kasashen Hausa amma duk da haka wasanninmu
na gargajiya kamar lokacin salla karama da babba, ko sallar
gani da kuma wasa kamun kifi na "Argungu" ana kokarin
inganta su da kawatasu. Wani abin lura ma shine yadda yanzu
aka tashi tsaye don inganta kayan kidan hauswa saboda su dace
da zamani. Wadannan kayan kida wadanda suka hada da Gar Kalangu,
Duman girke, Gangi, Dundufa, Shantu, Amada, Tandu da kidan
bi duk sun sami karbuwa ga 'ya'yan zamani bayan kuwa a shekarun
baya datta ne suka fi sha'awarsu. Haka kuma kidan goge, gurmi,
kuntigi da Garaya yar sun sami wani sabon matsayi musamman
idan aka dubi yadda kidan kukum tashe a yanzu
|
|