Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Wasannin Motsa Jiki Da Raye-Raye Da Wake-Wake 


 

WASANNIN MOTSA JIKI-RAYE-RAYE DA WAKE-WAKE
Masana suka ce Riyala wato wasannin motsa jiki na daga cikin tuwasun koyarwa. Su kuwa masu iya magana suka ce "taba kida taba karatu". Su yara ma'abota nishadi da wasanni ne saboda haka muddin aka ce karatun zasu rinka yi babu nishadi da wasanni to kuwa za'a taras aikin da ake koya masu basa fahimtarsa sosai. Aikin Riyala yawanci ana yinsa ne a hissa ta biyu da safe kafin yara su fita cin abincin tara. Masu tsarin ilmi sun yi bayanin cewa muddin ba wannan lokaci ne aka yi Riyala ba, to yara idan sun dawo daga cin abincin tara ba abinda zasu yi im banda barci.

Aikin Riyala suna da yawa, amma Malami shi ya fi sanin irin wasannin da ya dace da dalibansa. Duk wani wasa wanda zai cutar da yara bai kamata yara su yi shi ba. Wajibi ne Malamin makaranta ya kasance a filin wasa saboda shine jagorar yaran. Sai dai wani abin damuwa a yanzu Malaman makarantar boko suna nema suyi sakaci da riyala, sau da yawa sai aje filin wasa idan har anyi sa'a ana da filin a taras sai yaran ne zallansu ba wani Malami tare dasu suna wasan tamaula. Mafi yawan wadannan dalibai im banda fadace-fadace basa komai a tsakaninsu domin rashin ganin Malaminsu na kusa.

Wasanni irin namu na gargajiya suna da amfanin gaske a lokacin riyala. Irin wadannan wasanni masu motsa jiki akwai su Asaha ruwan tusntsaye da kuma Dan akuya na Damushere. Amma guje-guje da tsalle-tsalle sune mafi yawa daga cikin ayyukan riyala da ake yi a makarantun boko da na Islamiyya. Akwai kuma wasu wasannin da ake neman mantawa wanda ake kafa da'ira a rika yin wakar "Alal-kitkna mu tafa, alal-kitima mu tsalla, alal kitima-mu yi haka," da dai sauransu. Amma sai a kara kula ba'a son yin wasannin riyala cikin aji. Sai kuma wasannin raye-raye da wake-wake wadanda a kowane sako na kasar nan kuma kowace kabila tana da irin nata raye-raye da wake-waken. Alal misali idan Malam ya duba cikin littafin nan da Umaru Dembo Zariya ya wallafa mai suna "Wasannin yara" wanda aka buga a shekarar 1972 za'a ga yadda aka yi bayanin muhimman wasannin Hausawa na gargajiya kamar su na Kangal-kangal, Langa, Allan ba ku, ina aka saka, da kulli kucciya. Akwai kuma wasu wasannin da suma yanzu im banda a kauyuka ba'a yinsu irin su Malam na bakin kogi, Tayalo-Tayalo da Akube-kube kewano inji nufawan Kano. Duk wadannan wasanni an sani cewa samari da 'yan mata ne ke yinsu a kauyuka da birane, musamman a makarantun Firamare na jihohin Arewacin Nijeriya.

Wasan da yake kamar bako ne ga Hausawa shine wasan akube-kube kewano. Shi wannan wasa asalinsa Nufawa ne keyi wadanda suka gauraya da Hausawa a birnin Kano, kamar misalin a unguwar Ayagi da Tudun Nufawa, abin har ya zama jiki idan anyi haihuwa, wato ranar radin suna, sai 'yan mata su taru su dunguma suje wani babban filin wasa da aka samu amma kafin su isa sai su rika tafiya suna rera wannan waka kamar haka:

Akube-kube- kewano.
Akube-laji- kewano
Mun je mun dawo-kewano, Mun shawo rana- kewano.

Da an gama wannan wakar sai yara su sheka da gudu su hau wani dan tudu ko yaya yake suna cewa Allah ya raya wane ko wance, Allah yasa masha ruwa ne. Allah ya tsawaita yawancin kwanuka. Sai kuma a ci gaba da yin wakar da aka bayyana a sama har sai yaran sun koma gida. Wannan wasa duk da cewa cikin nufanci aka yi shi amma wasan yana jan hankalin dalibai wajen kara himma bisa ga aikin dake gabansu na makaranta, kuma yana daga cikin wasannin da dalibai 'yan mata ke sha'awa. Idan kuma Malamin makaranta tare da dalibai ya isa filin wasannin riyala da safe akwai wani wasa mai suna Alal-Kitima wanda dalibai ke sha'awa.Ita wakar Alal-kitima, waka ce wadda take tafiya da motsa jiki. Ga yadda ake yinta. Yara su kafa da'ira, Malam ko Malama yana tsakiya ko tana tsakiya, mai bada waka zai fara da cewa:

Alal-kitima- alal-kitima, sai sauran yaran dake da'ira har da Malam su amsa :
Alal-kitima-alal -kitima.
Alal-kitima mu tafa,
Alal-kitima mu tsalla
Alal-kitima mu yi haka,
Alal-kitima mu zauna
Alal-kitima mu mike.

Haka za'a ci gaba da yi har sai an kammala zagayen da'irar. Da an gama re wannan waka tare da motsa jiki, za'a ga yaran sun fara zufa. hakika wannan wasa babban Atisaye ne ga 'yan makaranta. Yawanci kuma 'yan mata sun fi son

wasangada irin su tayalo-Tayalo. Shi kuwa wasan Tayalo-tayalo, ba'a yin da'ira sai dai a hadu waje guda, sai wata yarinya daga cikin 'yan matan ta rika rera wakar su kuma sauran suna amsawa kamar haka:

Tayalo-tayalo (Amshi) Tayalo
fayalo kawata(Amashi) Tayalo
Ta yada taronta- " Tayalo
A gindin Marke- " Tayalo
Ba don ita ce ba- " Tayalo
Bazanbata ba- " Tayalo
Da nakasheshi- " Tayalo
Ammana bata shi-" Tayalo

Da an gama rera wannan waka sai kuma ayi tsalle ace Allah ya ka mu bikin wance. Sannan sai a koma aji ko kuma kowace ta koma gida abinta. Shi dai wannan wasa na Tayalo-tayalo ya kan yi tuni da nuna irin yadda yarinya zata sami kanta idan an yi mata aure a gidan mijinta. Bay an an gama wasan za'a ji 'yan mata na yiwa kansu fatan cewa Allah yasa kada su auri "Mai tazuge". A wajensu "Mai tazuge" tsoho ke nan.
Riyala ko Atisaye yana da muhimmancin gaske don haka ya kamata Malaman makaranta su kara himma wajen yinsa, kada malamai su sangarce suce ai wasa sai yara kawai, yaran suna bukatar mai masu jagora. Wassanninmu na gargajiya kuma idan har aka sake yaranmu suka manta da shi, kuma suka ga manyanmu basu dauke shi da daraja ba za'a wayi gari mu manta dasu baki daya, a barmu da surutai a gidajen rediyo, Telbijin da jaridu. Kowane abu na duniya yana da ginshiki, ginshikin al'adu na kunshe cikin jakar wasanni da raye-raye.




 
{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka [email protected]

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.