|
|
Makarantar
Boko
|
Tun kafm zuwan Turawa kasar nan Hausawa keda tsarinsu
na ilmi wanda Musulunci ya tanadar kamar yadda aka bayyana a
bay a. Saboda haka ba dai dai bane ace wai Nasara ne ya kawo
mana tsarin ilmi. Tarihi ya mmu cewa Sarki Mansa Musa da Sarki
Askiya Muhamma na daulolin Mali da Songhai sun burge duniya
ta hanyar yada ilmin tarihi, labarin kasa da ilmin addini tun
kafm ma turawa su fara tunanin fara mulkinsu na mallaka. Kafin
zuwan Mujaddadi Sahihu Usmanu Dan Fodiyo akwai wata makekiyar
jami'a a Tambatu ta kasar Mali ta yanzu wadda karfinta a wancan
lokacin dai dai yake da Jami'ar Oxford dake Ingila ko Havard
dake America. A wancan lokaci da ajamin Hausa da Fulatanci ake
bita, amma Larabci da Auzinanci suma harshe ne da ake bada darasi
dasu. Saboda haka ashe ba Bature bane ya fara kovawa Hausawa
ilmi ba. Da turawa suka zo sun same mu da da littattafanmu na
addini. dabi'u masu kyau da raye-raye da wake-wake.
Shi fannin ilmi wanda ake kira ilmin Boko da turawa suka zo
da shi ba wani sabon abu bane fil domin sauyin da aka samu shine
na harshen da ake koyarwa inda ake amfani da turanci. Sun kuma
kokarta sauya al'adun jama'a suna maye gurbinta da tasu. Amma
masana ilmi Musulmi dake Andalus wato (Spain) sune suka fara
bincike kan fannonin kimiyya, fasaha, labarin kasa da fannin
magunguna. Mun ki mu karbi salon ilmin da Nasara suka kawo da
ake kira ilmin Boko ne da wuri domin wadanda suka zo mana da
shi addininsu ya saba da namu. Ilmin Boko ya shigo kasar nan
ne ta hannun Mishan-Mishan. Hanyar da Mishan suka bi wajen yada
ilmin Boko ita ce tasa Hausawa gujewa tsarin saboda tilastawa
da suke yi wajen cusa ra'ayin addinin da suke tafe da shi. Wajibi
ne ga Malamin Makaranta ya san tarihin kasarsa da al'adunsa
don shima ya koyawa dalibansa.
Bambancin dake akwai tsakanin ilmin Muhammadiyya da ilmin Boko
shine ta hanyar da aka gabatar da ilmin, da kuma harshen da
ake amfani da shi wajen koyarwa. Ilmin Boko wanda a yanzu ake
kira ilmin Zamani da harshen turanci ake koyar da shi, amma
darussan da tsarin ilmin Boko ke dauke da shi akwaisu a tsarin
ilmin Musulunci. Kamar fannonin aikin gona, kimiyya, lissafi,
magunguna, da luggar Harsuna. Bambancin kawai shine ilmin Boko
yazo ne ta hannun turawa, shi kuwa ilmin Muhammadiyya yazo mana
ne ta hannun Musulmi larabawa. Haruffan da ake amfani dasu a
ilmin Boko daga haruffan Romawa aka samesu, amma haruffan ilmin
Muhammadiyya na larabci ne kuma sune haruffan da aka rubuta
Alkur'ani mai tsarki. Kamar yadda aka bayyana a wannan littafi
a baya cewa kowane fanni yana da Malamai masu koyar da fannonin
ilmin da mutun ya zaba, anyi bayanin dalibi na makarantar allo
da ilmin gafaka, haka shima tsarin ilmin Boko ya faro ne daga
Firamare zuwa jami'a. Saboda haka sai muyi tambayar cewa wanene
Malamin makarantar Boko?
|
|
{talla} |
|
|
|