|
Malamin Makaranta shine wanda ya koyi yadda zai
koyar da wasu. Su kuma masu koyo sune dalibai. Ilmi kamar yadda
masu hikima ke cewa Kogi ne, sai dai a dan debi abinda za'a
iya diba a bar sauran. Malamin Makarantar Boko shine wanda aka
koyawa fannonin da ake son dalibai su koya tun daga makaranrun
Firamare zuwa jami'a. Saboda haka Malamai sun kasu kashi dabam-daban.
Akwai Malaman Firamare, akwai na Sakandare, akwai na Jami'a.
Su kansu ' wadanda suka koyawa Malaman makarantun Firamare
yadda zasu koyar sun koya ne daga wasu Malaman. Kafin mutun
ya zama Malami sai ya san wani fannin da yake son kwarewa a
kansa daga cikin fannonin ilmi. Ana samun ilmi ne ta hanyar
koyon abu. Ilmi abune wanda idan aka same shi zai sauya wasu
daga cikin dabi'un wanda ya nemi ilmin. Kauda wannan abu shine
kauda jahilcinsa ke nan. yanzu misali idan yaro bai san wuta
ba, shi a ganinsa abar wasa ce. To idan ya kama hanya zuwa wajenta
aka kyale shi ya tsunduma hannusa ya ji ta kona shi gobe idan
ya ganta yasan wutace kuma zai guje ta. Wannan shine ilmi, ada
bai san wuta ba, bai kuma san zafinta ba. Amma da ya nemi ilminta
ya kuma samu sai dabi'arsa ta jahilci ta gushe. Wanda ya san
wani abu kuma ya kokarta nunawa danuwansa yadda wannan abu yake
don shima ya sami ilmi ya zama Malaminsa na wannan fannin da
ya sanar da shi. Shi ilmi wanda Malami ke koyarwa bai hada da
wanda aka halicci dan Adam da shi ba. Kamar ilmin tsotson nonon
uwa, ilmin jima'i wadannan fannoni ne da ba sai an koya ba,
domin ilmi ne da aka haifi dan Adam da shi. Ilmi kashi biyu
biyu, wanda zaka koya da kanka da wanda sai an koya maka. Ilmi
ya fi danko idan ana aiki da shi. Tilas kuwa sai da Malami sannan
za'a san yadda za'a yi aiki da ilmin. Koyon magana muna yara
kanana ba sai Malami ya koya mana ba, tilas mu koya da kanmu.
Haka kuma idan yaro ya tashi a cikin wata kabila misalin hausawa,
ya girma a cikinsu wajibi ne ya iya Hausa, ya iya sanya babbar
riga, rawani da wando buje da dai sauran al'adu irin na hausawa.
Amma idan dan Bahaushe ya tashi cikin wata kabila ba hausa ba
misali Yarabawa, zai tashi da koyon dabi'arsu da harshen yarabanci.
Malamin Makarantar Boko shine wanda ya sami horo a kolejin
horad da Malaman Makarnta hanyoyin da zai bi ya koyar da yara.
Kolejin horad da Malamai kashi uku ne. Akwai kolejin dake
horad da Malaman da zasu koyar a makarantun Firamare kawai
kuma wadanda ake kira Malamai masu daraja ta uku, ko ta biyu.
Akwai kuma babbar kolejin horon Malamai wadda ke horad da
Malaman da zasu koyar a makarantun gaba da Firamare wadanda
ake kira sakandare, kuma sune masu daraja ta daya ko kuma
babbar shaidar koyarwa ta NCE. Sai kashi na uku kuma na karshe
wati Jami'a inda aka ware fanni na musamman kan karantarwa,
sanin dabi'ar yara da halayensu, hanyar yadda za'a koyi abu
sannan a koyar. Malaman da suka sami horonsu na koyarwa a
Jami'a sune suke koyarwa a kolejojin horon Malamai, Sakandarori
da ita kanta Jami'ar. Malamin makarantar Boko ya san fannonin
biyar zuwa shida wadanda ake koyawa yara tun daga Firamare
zuwa Sakandare. Wadannan fannoni kuwa sun hada da Turanci,
lissafi, koyar da rubutu da karatu cikin harshen Hausa, kiwon
lafiya da Riyala wato ayyukan motsa jiki. Irin wadannan Malaman
ne suke koyarwa a Makarantun Firamare. Ma'aikatun ilmi na
jihohi da kananan hukumomi ne ke daukar nauyin biyansu albashinsu.
Kuma sune ke samar da kayan aiki da littattafan da Malamai
ke amfani dasu don koyawa yara. Sai dai yanzu saboda karancin
kudi iyayen yara ne ke daukar mafi yawa daga cikin dawainiyar
harkokin karatun 'ya'yansu amma banda biyan albashin Malamai.
Malamin makaranta shine wanda ya san abinda zai koyar, shine
jagorar yara wajen ci gaban rayuwarsu ta duniya, yana da tsafta,
baya rena al'adunmu na gargajiya. Malamin Makaranta baya fushi,
bashi da girman, baya rena jama'a, bai kuma dauki kansa yafi
kowa sani ba, kullum a cikin fara'a za'a ganshi. Yara sune
abokansa, kullum a shirye yake ya taimakawa dalibansa idan
suna cikin wata matsala. Malam sai ka duba ko kuma ki duba
ki gani ko ana da wadannan halayen da aka lissafa a sama.
Koma Baya
|
|