Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Makarantar Alkura'ani 


  Makarantun Alkur'ani a kasar Hausa sun kasu kashi biyu. Kashi na farko shine inda ake koyawa yara karatun Alkur'ani kawai ba tare da hadda ba. Kashi na biyu kuwa shine inda ake karantarwa hade da hadda. Bari mu fara da kashi na farko domin shine matakin farko, kuma shine ya fi yawa a duk fadin kasar Hausa. Ana sa yaro ko yarinyu Makarantar Alkur'ani ne lokacin da suka cika shekara biyar. Ana kiran irin wannan Makaranta da sunan Makarantar Allo, domin a cikinta ne yara ke koyon karatun Alkur'ani kuma a kan Alluna ake koya masu rubutu da ka m t u. Wadannan makarantu basu da iyaka domin da wuya a sami magidanUi rnnsu 'ya'ya da zasu barsu hakabatareda ansakasu a Makarantar Allo ba.

Malamin da yacancantayabude Makarantar Allo shine wanda zai iya karanta Alkurani dukkansa kuma ingataccen karatu, ya kuma haddace a kalla izifi daya, misali daga surar Sabbi zuwa Nasi. Yadda ake karantarwar kuwa shine Malami zai fara rubutawa yara haruffan Alif, Ba. Ja, Da, ba tare da wasali ba. Idan yaro ya sansu sai a rubuta masa surar Fatiha, ita ma bada ' wasali ba, sannan a koya masa fadar haruffanta har ya sansu. Daga nan sai aci gaba zuwa surar Nasi, sai Falaki, sannan Kulhuwa, sai Tabat yada, sai Iza ja'a, haka dai har sai dalibi ya kai surar Wailul Likulli. Daga nan sai a sake dawo da dalibi kasa a rubuta masa Fatiha da Wasulla ana koya masa yadda ake tada baki har sai ya san duk surorin nan ya kuma haddace su. Daga nan sai ayi ta rubutawa dalibi surori ana koya masa tare da hadda har sai ya kai Sabbih. galibi daga nan ne dalibi zai daina hadda sai ya yi ta karanta surori bayan an rubuta masa aAllo har sai ya kai Amma. Hakanan dai tafiya sai ta mika ya yi tayi har ya sauke Alkur'ani. A tsakanin wannan lokaci ne dalibi zai koyi rubutu da kansa bayan ya gama sai Malaminsa yayi masa abinda ake kira Safi, ya huta ke nan dawahalar rubutu.

Wannan hanya takan dauki dalibi kimanin shekaru hudu ko fiye da haka kafin ya sauke Alkur'ani. Akwai wasu surori ko hizifai da iadan dalibi ya kai garesu Malami yakan nemi mahaifin yaron da yayi masa sadaka ta abinci ko ya yanka Akuya ko Rago. Bisa ga al'ada wannan sadaka gidan Malami ake kaiwa. Dalilan da aka bayar na kaiwa Malami sadaka shine domin ba kasafai iyayen vara ke baiwa Malaman Allo Iadan karantarwar da suke yiwa 'ya'yansu ba. Malam kan ce wai idan ba'a yi wannan sadakr ba dalibi na zama wawa ko dakiki. Idan yaro ya sauke Alkur'ani sai kuma mahaifinsa ya shirya babban taro ko liyafa inda ake gayyatar 'yanuwa da abokan arziki su zo su albarkaci wannan yaro. Ana cikawa Malamin yaron aljihunsa da kudi.
 
{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka [email protected]

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.