Hausa Hausa English
Wakokin Hausa

Chat Room
Check your mai

Classified Ad

Jaridu


Mahada

 

 

 

 

Horo Maitsanani 



 
Masu iya magana suka ce "gora maganin mai kwarin kai", amma a fanni irin na koyarwa wannan karin magana ba zai sami wurin zama ba. Yawan duka da yawan zagi ba abinda zai kawo im banda taurin kai, rashin biyayya da kore sha'awar nazari daga zuciyar mai bidar ilmi.
A makarantun mu na gargajiya wato makarantun allo, babu wata hanyar horon yara da ta wuce yin amfani da bulala. Amma masana kimiyyar halayyar lan Adam sun yi nazarin cewa yawan duka da zare idanu basa kawo ladabi da . ayya sai dai aji tsoron Malami. Haka kuma yawan duka da zare idanu basa taimakawa dalibai su fahimci abinda ake koya masu. Dalilin haka ne cikin 1953 aka kaddamar da sabuwar hanyar koyar da yara karatun allo don ta dace da zamani. Shirin ya tanadi yadda dalibai zasu rika zama kan bencina, sannan a ginabakin allo inda Malami zai rika rubuta haruffa. Allon na iya kasancewa na katako ko sumunti. Irin wadannan makarantu sune ake kira makarantun Islamiyya. Ana koyar da karatun Al-kur'ani mai tsarki kamar yadda ya dace tare da koyar da fannin ibada. Wannan hanya ta taimaka kwarai wajen baiwa Malami damar halartar kowane dalibi daga cikin dalibansa dake cikin aji musamman idan an nemi taimakonsa. Duk da haka wasu basu sun ki yarda da wannan sabuwar hanya ta koyarwa.

Tsabar gaskiya ita ce duk Malamin da yake son dalibansa su fahimci aikin da yake koyarwa to, ya nisanci yin amfani da tsumangiya. Hanyoyin horon dalibai suna da yawa, kuma ya kamata Malamin makaranta ya sansu don kaucewa yin amfani da tsumangiya wadda hakan bai dace a fannin koyar da dalibai ba musamman a makarantun boko. Wasu na cewa wai ai yaranmu basu biyuwa sai da duka. Wannan ba haka bane, yawan duka babu abinda yake karawa sai sangarta yara su bi uwa duniya suna yin barace-barace, wasu kuma su zama manyan 'yan iska. Idan kaje tashoshin mota sune zaka rika gani sun zama abin tausayi, babu cin yau balle na gobe, daga karshe sai su shiga yin sace-sace. Don haka babban kuskure ga Malaman makarantu su makalewa tafarkin yin amfani da tusmangiya. Ya kamata a koma hanyar yin amfani da lallashi. Alal hakika, bada yara ga Malaman allo tun daga farko suna yawo bashi da fa'ida im banda kangara da ake jawowa yaran. Sau da yawa idan irin wadannan Malamai suka debi yara sai suce zasu gabas bidar karatu, amma abin lura shine babu abinda ya dami Malamin wajen lura da yaran ko suna cin abinci ko kuwa a'a, hatta ma lafiyarsu ba abinda ya sha mar kai. Irin wadannan daliban ne motoci ke bugewa a titunan biranen kasar nan. Su irin wadannan Malumma sune kuma suka fi yin amfani da bulala wajen horon dalibai, daga karshe ba karatun ba ladabi da biyayya da iyaye ke bukata. Don haka Malamin makarantar Allo, Islamiyya da boko a daina yin bulala, a koma ga hanyar yin lallashi da tintibar iyaye. Idan anyi dace sai a dace.
 
{talla}

Littatafan Hausa

 
Gidajen Rediyo Hausa

 

 

       
 

Mohammed Hashim Gumel ya tsara ya gina wannan shafi. Kofar mu a bude take bisa duk wasu shawarwari da kuma ra'ayoyinku, kan wannan fili, da kuma irin abinda kuke so mu rika wallafawa."Gyara kayanka bai zama sauke muraba ba." Ana iya aiko mana da wasika ta layi kamar haka [email protected]

@Gumel.com 1998 Wannan fili an kareshi da dokar wallafawa, a nemi izzini kafin amfani da kayan mu.