|
|
Hedimasta
|
Hedimasta, shine shugaban Malamai a makarantar Boko, kuma shine
idon hukuma da iyayen yara a makaranta. Shine turken Makaranta
idan ya tsaya Makaranta ta tsaya, idan yayi sakaci Makaranta
ta rushe. Hedimasta mutun ne na gari mai cikakken hadin kai
da sauran Malamai da shugabannin gari. Hedi masta mai kwazo
ne da sanin ya kamata. Yana ilmi daidai gwargwadon yadda ake
bukatar kowane Malamin makaranta ya samu. Ya iya tsara ayyukansa
sy tafi kamar yadda ya kamata. Shugabannin gari na neman shawara
daga wurinsa. Ya kan riga kowa zuwa Makaranta don tabbatar da
tsaftar azuzuwa kafin yara su fara aiki a cikinsu. Dagewar Hedimasta
ce zata sa malami su rika zuwa wurin aiki cikin lokaci da tabbatar
da ganin anyi kiran suna don a gane daliban da suka makara ko
kuma suka ki zuwa Makarnta. Aikin Hedimasta ne ya san irin horon
da za'a yiwa yara, kada ayi horon da zai cutar da yaro, kuma
ya haddasa fitina tsakaninsa da iyayen yara ko Malamai. Aikinsa
ne ya kare mutuncin Malamai da Makarantarsa. A kowace safiya
aikin Hedimasta ne ya tabbatar Malamai sun shirya ayyukansu
kafin su fara aiki.
Saboda irin girman da Hedimasta ke da shi a idanun jama'a da
shugabanni ashe kuwa ya kamata ace sai wanda keda halayen da
aka bayyana na gari ne ya kamata a baiwa matsayin Hedimasta.
Bayan ya sami horonsa a kolejin horon Malamai, wanda ya kamata
ya zama Hedimasta shine Malami mai kwazo, kishin kasa, mai tsafta,
mai kwadayin neman ilmi, mai rikon Amana da zumunci da sanin
ya kamata. Galibi a kan so a baiwa dattijo wannan matsayi na
Hedimasta, amma idan aka sami matashi mai halaye na gari da
ilmi kamar yadda ya dace babu laifl a bashi matsayin Hedimasta.
Yawan dadewa a sana'ar koyarwa tare da yin aiki tukuru suna
taimakawa a baiwa Malamin Makaranta Hedimasta.A kalla ya kamata
ace wanda zai sami matsayin Hedimasta ya kasance yana takardar
shaidar malanta mai daraja ta biyu. A yanzu da yake karatun
boko ya bunkasa ana baiwa wadanda keda digiri ko takardar shaidar
NCE matsayin Hedimasta bayan sun dan yi aikin koyarwa har tsahon
shekaru biyu ko daya. Amma kada a manta da cewa da tsohuwar
zuma ake magani domin Malaman da suka jima suna aikin koyarwa
a makarantu, kuma suka nuna kwazo da sha'awar koyarwar, suma
ya kamata a tuna da irinsu wajen basu matsayin Hedimasta bisa
sharadin zasu kokarta cin jarrabawar neman shaida mai daraja
ta biyu. Muhimman abubuwan kulawa wajen zabar wanda zai zama
Hedimasta sun hada da da'ar da mutum ke da ita, ilmi da hazakarsa
tare da sanin mutuncin jama'a. |
|
{talla} |
|
|
|