|
Aikin Malamin Makaranta ne yayi amfani da hanyar
koyarwar da aka koya masa a Kolejin horon Malamai saboda hanyar
koyarwa ita ce jagorar Malami ga cimma burinsa na fahimtar da
dalibai. Hanyar ba ita ce nasarar Malami ba, sanin hanyar da
yadda za'a yi amfani da ita. Aikin Malami ne ya tambayi kansa
shin \me zai koyar ne, ta yaya zai koyar da wannan abu, kuma
don me zai koyar da wannan abin? Ya kamata Malamin makaranta
ya sani cewa ba daukar Alii a tsaya a cikin aji shine Malanta
ba, shin Malamin ya san abinda zai koyaj da kuma yadda za'a
koyar? Aikin Malamin Makaranta ne ya san inn fa'ida da rashinta
da za'a samu idan an koyar da wani abu. Ba aikin Malamin Makafanta
bane ya taje ciko ya daure ciki, da sanya katon
Fantalo yace shi Tica bane domin yara zasu yi koyi da duk
abinda suka ga yayi. Wajibi ne Malamin Makaranta ya kokarta
amsa sunansa ta hanyar nuna aiki na gari, sanya sutura ta
gari, biyayya ga na gaba da kyawawan al'adun za'a koyawa yara.
Lokacin da Malamin Makaranta ke tsaye a cikin aji, kuma aka
yi dace yara duk suna saurarensa, sai yayi matukar kokarinsa
ya ga daliban sun fahimci abinda yake koyarwa. Koyarwa irin
ta hadda yanzu bata da fa'ida ga yaranmu. Alal misali kada
Malamin makaranta ya rubuta wadannan kalmomin a kan allo ya
baiwa dalibansa umarnin su haddace kafm gobe. Kalmomin da
za'a bada misali dasu a hissar turanci sune: A noun, a Verb,
Pronoun da sauransu, wato idan Malami yace a haddace masa
tuwasun magana na turanci da ake kira "parts of speech",
karshen abin shine sai yara su haddace amma basu san abinda
suka haddace ba. Kamata yayi Malamin makaranta ya kokarta
koyar da darasin a aikace. Aikin koyarwa baya bukatar raggo,
baya bukatar yawan zama a kan kujera ko tebur sai a lokacin
da zai duba ayyukan da yaran suka yi. Maimakon tilastawa dalibai
su haddace tuwasun maganar turanci a hissar turanci da aka
bada misali Malamin na iya saukaka darasin ta bin wannan hanyar:
Malami: Sai ya nuna wani yaro a cikin aji yace yaya sunanka?
Yaro: Sunana Ado
Malami: Da ka tashi daga Makaranta ina zaka?
Yaro: Gida za ni.
Sai Malami ya rubuta wadannan kalmomin a kan allo wato ADO
da GIDA. Sai yajuya wajen yara ya yr rnasu nuni da cewar komai
a duniya yana da suna,-kun ga ADO suna ne na wancan yaron,
sai ya nuna shi. Kuma GIDA suna ne na wurin da muke kwana
da harkokin rayuwarmu na yau da kullun. To, su wadannan sunaye
suna karkashin "NOUN" daya daga cikin tuwasun magana
takwas na harshen turanci. Sai Malamin yaci gaba da yin haka
wajen koyar da sauran tuwasun maganar, ta haka yaran zasu
fahimci aikin fiye da zare masu ido da yin bulala a hannu
a tilasta masu sai sun haddace. A fannin koyar da harshen
Hausa ma haka ya kamata Malami ya rika yi don saukakawa, domin
shima harshen Hausa yana da wahalar koyo da koyarwa kamar
sauran harsuna. Kada malamin Makaranta ya dogara da hanyar
koyarwa guda daya, idan ya gwada wannan yaga bai sami nasara
ba sai kuma a wani darasin ya sake wata hanyar. Kullum Malamin
Makaranta a neman ilmi yake, shi yasa ake son Malami ya rika
halartar dakin karatu wato 'Library' don fadada saninsa. Yin
'haka zai taimakawa Malami saboda wani lokaci idan Malami
yayi kuskure.
kuma yara suka je dakin karatu 'Library' suka bincika su
gano kuskuren sai su nemi wulakanta Malamin, su dauka bai
san abinda yake koyarwa. Aikin Malamin Makaranta ne ya san
yadda ake tsara aikin da za'a koyar wanda shima aka koya masa
a kolejin horon Malamai.
|
|