|
|
Aiki
A Karkara
|
Kamar yadda aka sami wahala kafin ilmin Boko ya
sami karbuwa a biranen jihohin Arewa, haka abin ya kasance a
kauyuka. lyaye suka rika boye 'ya'yansu basa son su kaisu Makarnta,
sun gwammace su bar 'ya'yansu suyi masu aikin gona. Wasu kuma
a tura su Makarntun Allo daga nan ne wasu ke sullebewa su gudu
zuwa birane. Kamar yadda aka yi bayanin tsarin Makarantun Allo
a baya za'a fahimci cewa ba'a yi maganar ci rani da dalibai
ke barin kayuka zuwa birane ba. Shi dai ci rani baya kara komai
sai lalacewar dalibai. Mafi yawa daga cikin daliban da suke
zuwa birane ci rani basa yin karatun sai dai neman abinda zasu
ci da wanda zasu kaiwa malam gida. Yawon ci rani dai ya sami
asali ne daga matasa wadanda bayan sun kammala aikin gona suke
kokarin shiga birane don kadar raba, idan damuna ta fadi su
koma kauyu-kansu. A shekarun baya, aPamarin yana da dan kyau
ba kamar yanzu ba. A baya can ana samun albarkar gona mai yawa,
kuma kayan abinci bashi da tsada. Da kudin da manomi ya saida
amfanin gonarsa ne yake yiwa 'ya'yansa da matansa sutura da
sayen kayan abinci. Shi yasa basa son barin 'ya'yansu zuwa Makaranta
don kada a rage masu ma'aikata a gonakinsu. Halin rayuwa a karkara
a yanzu ta lalace saboda tabarbarewar tattalin arziki da harkokin
noma. Babu isassun kayan abinci kamar da. Babu wuraren shakatawa
a karkara kamar yadda ake dasu a birane.
Bayan da hukumomi suka sami nasarar wayar da kan jama'a a kauyuka
wajen tura 'ya'yansu makarantu sai wasu matsalolin suka taso.
Wadannan matsaloli kuwa sun hada da gina makarantu, samar da
kayan aiki, Malaman da zasu koyar da kuma ayyukan yi bayan yaran
sun kammala makaranta. Idan ya rage watanni uku daliban Makarantun
horad da Malamai su kammala karatunsu na TITISI, babu abinda
yake ran Malami sai tunanin inda za'a kaishi yayi aikin koyarwa.
Amma saboda rashin kayan jin dadin rayuwa a kauyuka mafi yawa
daga cikin Malaman makarantun Boko basa son zuwa kauye don su
koyar. Shi yasa halin da makarantun boko a kauyuka suke ciki
bashi da kyaun gani. Babu isassun kayan aiki a makarantun kauyuka,
babu abin zama, babu gidajen kwanan Malamai da dai sauransu.
Gashi kuma idan aka yi la'akari da yawan haihuwa da ake yi a
kauyuka za'a ga cewa ana bukatar yin gyara sosai-da sosai a
makarntun boko dake karkara don a kwadaitawa Malamai zuwa kauye
su koyar. Malaman boko da suka amince da zuwa kauye su koyar
suna haduwa da matsalar abinci, shi yasa ake ganin zai yi kyau
Malamin Makarantar boko a kauye yayi kokarin koyon yadda ake
dafa abinci idan bashi da mata wadda zata dafa masa. Giggina
Makarantun da aka fara yi a kauyuka, ya kamata aci gaba da yi,
sannan a gyara wadanda ake dasu don samar da gurbin wasu daliban.
Majalisun kananan hukumomi su inganta hanyar da suke bi wajen
samar da kayan aiki a makarantun karkara ta yadda dalibai da
su kansu Malamai zasu ji dadin yin nazari. Sai kuma maganar
samun Malaman da zasu koyar. Kamar yadda aka bayyana a baya
cewa daliban kolejojin horon Malamai basa son zuwa kauye ya
kamata a gyara wannan matsayi domin rashin zuwa kauyen da Malamai
keyi ya faru ne saboda rashin hanyoyin jin dadin rayuwa kamar
ta birni. Su kansu daliban da suka fito daga kauyuka basa son
komawa can suyi aikin koyarwa saboda wadannan matsaloli da aka
bayyana.
Shawarar da za'a ba Malamin makarantar boko ita ce ya hakura
ya tafl kauye ya koyar duk da cewa akwai matsaloli. Gefe guda
kuma hukumomin da abin ya shafa su dukufa wajen neman hanyoyin
kyautata rayuwar karkara. Tunda matsaloli ne ke hana Malamai
zuwa kauyuka ya kamata a kokarta kauda wadannan matsalolin.
A samar da gidajen kwanan Malamai, kekunan hawa da kyautata
albashin Malamai tare da biyansu a kan lokaci. Malamin makaranta
idan yayi hakuri ya tafi kauye yana koyarwa bayan ya shekara
biyu zuwa uku sai a sauya masa wuri zuwa birni, idan kuma yaji
dadin zama a kauyen sai a kyale shi a can. Muddin Malamin makaranta
yace ba zai fita kauye ya koyar ba waye ke nan zai koyawa 'ya'yanmu
dake kauyuka ilmi? Mafi yawa daga cikin kasashen da suka ci
gaba a duniya Malaman Makarantunsu duk a karkara suke aikin
koyarwa, kuma ana kyautata masu sosai yadda ya kamata. |
|
{talla} |
|
|
|