|
Dawainiyar Bincike, sirke da Kimiyya
ta kan jirkita ta kuma juya halin ilmin halittu da na tasawirorinsu.
Dauki misalin nazarin Sararin Samaniya ba tare da Kimiyya
ba; sannan ka gwada shi da nazarin da aka yi shi tare da Kimiyya
da irin sabbin damar da ta kawo na saukakar da Bincike
da fahimtar maanarsa.
Daya daga cikin baiwoyin da Allah (swt) Ya ba wa wasu
mutane, ita ce baiwar Bincike da son bin kwakwaf,
wad'anda himmarsu da kwadayin neman saninsu suke yi
masu jagora a kan wannan darika ta neman ilmi. Sakamakon
wannan fafutuka tasu ita ce ilahirin riba da ci-gaban 'Dan-Adam,
tun daga farkon lokaci. A cikin wannan dawainiya, mutum
ya kan shirya halayen tafiye-tafiye da burin kosarda
bukatunsa; ko don kan sa, ko jamaarsa, ko don alummar
'Dan-Adam gaba-dayanta. Yawon duniya, harin yaki
don ganima, tijara, farauta, hijira, hajji, duk dawainiya
ne da 'Dan-Adam yake yi don biyan bukatunsa, ko kuma cika
umarnin addini ko na jamaa. A kowane hali na tafiye-tafiye,
sabon ilmi yakan wanzarda kan sa a cikinta, in dai an yi nazari
mai zurfi tare da auna manufar tafiyar ita kan ta.
A cikin tarihi, mun karanta labaran mashahuran mutane wad'anda
suka yi d'awainiya a rayuwarsu don binciken sabon ilmi; kuma
yawanci sukan tunkari matsaloli masu wahala a cikin wad'annan
tafiye-tafiye nasu. Labaran mutane irinsu Alekzandara-za-gret
(wanda wasu ke kuskurarren zaton shine Zurqallaini), Kolumbas,
Vasco da Gama, Agha-Khan da sauransu, duk labarai ne na mabudan
ilmi da gwagwarmaya iri-iri. Rayuwar Manzon Allah, Muhammad
(saw), da ta yawancin annabawa da waliyan addinai, kyawawan
misalai ne na gwagwarmayar 'Dan-Adam da sadaukarwa don ilmantarwa.
Haka muka ga bazuwar addinin musulunci ta zama mabudin
ilmi iri-iri a koina a duniya, bayan kafa addinin shi
kan sa. Idan muka karanta ayoyin Kimiyya a cikin Al-Qur'ani
mai-tsarki, muka kuma yi nazari a kansu, ba shakka za a fahimci
abin da nake nufi anan. Ashe dai tarihin 'Dan-Adam gaba dayansa,
tafiyace cikin wannan himma ta neman ilmi; tun ana yin ta
a kas, ta koma kan dabbobin hawa, sannan a jirgin ruwa,
har ga shi an kai shiga ko aika kumbuna masu ziyara da shawagi
a Sararin Samaniya. Duk wad'annan ci-gaba na ababan sufuri,
sakamakon bincike ne da Kimiyya, bayan alhairi na ilmin da
aka tarar a dukkanin guraren da aka je.
'Dan-Adam ya fara d'awainiyar bincikensa ne tun ya na dan-jariri
a doron wannan yar duniya tamu wadda Al-Qur'ani yake
kira, Ard, wadda kuma da can mutum ya zaci ba koina
a Sararin Samaniyar sai ita. Tun ya na zaton cewar daben
turbaya ce a shifide a mike tamkar
darduma, har dai ya fahimci cewar a kewaye take kuma a dunk'ule
take tana lilo ita kadai tamkar tamaular da aka lula
sama. Da ya fahimci wannan, sai 'Dan-Adam, ya shiga d'awainiyar
binciken ilmin kasashe, tekuna da koguna, da duwatsun
dake kan doronta, muhallinsu da kuma dalilan da suka sa ba
sa fadowa. A cikin wannan tafiya ta bincike, sai ya
fara lura da irin mutane, dabbobi da tsirannin dake cikinta,
kuma wannan fafutukar har yanzu ba ta kare a gunsa ba.
'Dan-Adam ya na dada tsufa, bukatun rayuwarsa da kuma
tilastuwar bincike don kosardasu, suna k'ara yawa. Idan
muka tuna, tun kafin balagarsa ne, mutum ya fahimci muhimmancin
neman sabbin muhallai wad'anda zai iya bakunta koma
ya mallake ya kuma mamaye.
Don hakane ma ya shiga binciken budurwoyin k'asashe inda
zai koma ya kafa rayuwarsa da kuma ta zurioinsa.
Wannan ta baza 'Dan-Adam kusan koina a kan doron duniyarsa,
ta kuma haifarda sabon ilmi da muhimmancin albarkar k'asa,
wadda ita kuma ta zama sabon dalilin wasu tafiye-tafiyen,
yake-yake, hijira da tijara. Cikin lokaci, sai
baki a wasu gurare, suka kai sabbin abinci, aladu,
ilmi, siyaysa -har ma da addinai- ga k'asashe da alumun
da suka bakunta. Har-wa-yau kuma, a wasu guraren, bakin
suka maishesu mazauninsu ko guraren huldarsu, koma a
yawancin lokatai, na mallakarsu.
Zamanin da mutum yake kan gayar bincikensa, wannan duniya,
ba shakka, ta ga canje-canje irin yadda ba za a sake gani
ba. Daga dalilan kosarda kishirwar ilmi, har aka
kai na kosarda bukatun rayuwa da danniya, har sai da
bako yazo yafi dan-gari bajinta a garinsu. Turawa,
Larabawa -sannan mutanen Sin- duk sun yi rawar ganinsu a wannan
harka ta baza bazarsu duk inda fuka-fukansu zasu iya zuwa.
Ba shakka, har izuwa yau, kurar da suka tayar a gurare
masu nisa ba ta kare bajewa ba. Duk wannan a sunan binciken
sabbin tasawirori, gabobi da iyaku; neman ilmi,
dukiya da sabbin muhallai. Amma duk da haka, tasirin wannan
d'awainiya ta bincike ba ta raunana ba, illa ma karfafa
da tayi cikin imanin cewar ba ta da bambanci da makomar
|
|